Take a fresh look at your lifestyle.

Kenya Ta Musanta Ikirarin Murabus Din ‘Yan Sanda A Haiti

96

Babban jami’in ‘yan sandan Kenya ya musanta rahotannin da ke cewa jami’an da ke aikin wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa na Majalisar Dinkin Duniya dake marawa kasar Haiti baya sun shafe watanni uku ba a biya su albashi ba.

 

Sufeto Janar na ‘yan sanda, Douglas Kanja, a ranar Alhamis ya ce an biya jami’an Haiti albashi “har zuwa karshen Oktoba.”

 

Yana mai mayar da martani ne ga rahotannin da kafafen yada labarai na kasar Kenya suka bayar, inda suka ambato jami’an da aka tura wadanda suka koka da cewa ba a biya su albashi ba tsawon watanni uku.

 

Kenya na jagorantar tawagar ‘yan sandan kasashen waje a kasar Caribbean mai fama da rikici domin taimakawa wajen dakile tashe tashen hankula.

 

Jami’an Kenya da aka tura a watan Yuni sun kasance karo na hudu da manyan sojoji ko ‘yan sanda na kasashen waje suka shiga Haiti.

 

Yayin da wasu ‘yan kasar Haiti ke maraba da su, wasu kuwa na kallon rundunar da taka tsantsan, ganin cewa tsoma bakin da aka yi a baya.

 

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a tsakanin 2004-2017 ta fuskanci zarge-zargen cin zarafi da shigar da cutar kwalara, wadda ta kashe kusan mutane 10,000.

 

Rahoton kudi daga baitul malin Kenya ya nuna cewa Kenya ta kashe sama da shilling na Kenya biliyan biyu ($15 miliyan) don aikin a lokacin da take jiran mayar da kudaden da Majalisar Dinkin Duniya ta biya.

 

“Wannan kudaden da muke kashewa a madadin Majalisar Dinkin Duniya, mu ne ke biyan kudin don haka kudaden suna fitowa daga asusun mu saboda wadannan jami’an mu ne,” in ji Ministan Baitulmali John Mbadi.

 

Fiye da mutane 4,500 ne aka bayar da rahoton kashewa a Haiti a bana, yayin da wasu 2,060 suka jikkata, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

 

Rikicin kungiyoyin ya kuma raba kimanin mutane 700,000 da muhallansu a cikin ‘yan shekarun nan, yayin da ‘yan bindiga ke konawa tare da yin garkuwa da jama’a a wani yunkuri na mallakar karin yankuna.

 

Jama’a na ci gaba da sukar tawagar da Kenya ke jagoranta, tare da yin la’akari da cewa ‘yan sanda ba su kwace iko da sansanonin ‘yan kungiyar ba, ko kuma kama wasu shugabannin kungiyoyin.

 

Rikicin kungiyoyin ya kara kamari ne a watan da ya gabata yayin da Amurka da sauran kasashe ke yunkurin kafa tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, lura da cewa tawagar da Kenya ke jagoranta a halin yanzu ba ta da wadata da kudade.

 

 

Africanews/Ladan Nasidi.

Comments are closed.