Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya isa birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa domin ziyarar aiki a kasar.
Ya sauka a filin jirgin sama na Al Maktoum, Dubai, da sanyin safiyar Asabar.
Jakadan kasar UAE a Najeriya Salem Saeed Al Shamsi ne ya tarbe shi da isarsa; Daraktan Sashen Harkokin Afirka, Ma’aikatar Harkokin Waje, UAE, Ambasada Salem Al Jabri da Ambasada Beatrice Ikeku Thomas, mai kula da harkokin ofishin jakadancin Najeriya a Hadaddiyar Daular Larabawa, UAE.
Mataimakin shugaban kasar ya je Dubai ne a madadin shugaban kasa Bola Tinubu, domin kaddamar da jirgin ruwan Oriental Energy na zamani na dala miliyan 315 na Lodin kayayyaki,Tarawa da saukewa (FPSO).
Karanta Haka: VP Shettima Zai wakilci Shugaban Kasa Tinubu A Kaddamar da Kamfanonin Mai
A cikin tawagar mataimakin shugaban kasa akwai gwamnonin jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum da na jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, da kuma mai ba shi shawara na musamman kan ayyuka, Dakta Aliyu Moddibo.
Ladan Nasidi.