Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnan Kano Ya Nada Tsohon Shugaban Ma’aikata A Matsayin Sakataren Majalisar Shura

202

A ranar Juma’a ne Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya sanar da nadin tsohon shugaban ma’aikatan fadarsa (CoS), Shehu Wada Sagagi, a matsayin sakataren majalisar shura ta jihar Kano.

 

Gwamnan ya nada Farfesa Shehu Galadanci a matsayin shugaba,Farfesa Muhammad Sani Zahraddeen ya zama mataimakin shugaban majalisar Shura mai wakilai 46.

 

Majalisar Shura ita ce koli ta zamantakewa da addini kuma ana sa ran za ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba a fadin jihar.

 

Sauran manyan ‘yan majalisar Shura sun hada da Sheikh Abdulwahhab Abdallah, Sheikh Karibullah Nasiru Kabara, Dr. Bashir Aliyu Umar da Sheikh Tijjani Bala Kalarawi.

 

Gwamnan a cikin wata sanarwa da kakakin shi Sunusi Bature ya fitar, ya ce majalisar ta kunshi fitattun malaman addinin musulunci, manyan malamai, da kuma fitattun shugabannin al’umma.

 

“Shahararrun mambobi sun hada da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da Farfesa Salisu Shehu, da Dr. Muhammad Borodo, da Khalifa Hassan Kafinga, da sauransu.

 

“Sakataren majalisar kuma shugaban sakatariya, Gani Shehu Wada Sagagi, zai sa ido a kan ayyukanta don tabbatar da inganci da daidaitawa.

 

Sanarwar ta ce “Wannan shiri zai nufin samar da hadin gwiwa tsakanin gwamnati da masu ruwa da tsaki, na nuni da kudurin Gwamna Yusuf na tabbatar da gudanar da mulki tare da mutunta cibiyoyin al’adu da addini na Kano.”

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.