Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin Jihar Kebbi Ta kaddamar Da Shirin Rabon Kayan Masarufi kyauta Ga Al’ummar Jihar.

Binta Aliyu,Kebbi.

86

Gwamnan Jihar kebbi, Dakta Nasir Idris ya kaddamar da rabon abinci kyauta ga al’ummar Jihar don rage radadin talauci da Jama’a ke ciki.

 

Gwamna Nasir Idris ya kuma yayi alkawarin ‘hukumta’ duk wani Jami’in Gwamnati da aka samu ya karkatar da kayan abincin zuwa Gidaje su.

 

“wannan abincin daga asusun Gwamnatin jihar ne, amma gwamnatin tarraya ta fara turo nata abincin, in sun kammala isowa jihar za’a raba wa Al’umma”  in ji Gwamna.

 

Gwamnan ya kuma yi Kira ga masu ganin rashin gyara hanyar garin Zuru a Matsayin siyasa ce, yace “ wannan hanyar gwamnatin taraya ta bada kwangilar gina ta, shi yasa Gwamnatin jihar bata yi katsalandan akan aiyokan hanyar ba”.

 

Gwamna Nasir Idris ya kuma nada kwamitin da zasu raba abincin Wanda ya hada da yan- majalisu da Shugabanin kananan hukumomi da Jami’an tsaro da kuma sarakunan gargajiya.

 

 

Binta Aliyu.

Comments are closed.