Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Jam’iyyar APC Ya Yabi Nasarar Gyaran Tattalin Arzikin Shugaba Tinubu

191

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Dakta Abdullahi Ganduje ya yaba da sauye-sauyen tattalin arziki da shugaba Bola Tinubu ya bullo da shi inda ya bayyana cewa tuni aka fara samun sakamako mai kyau.

 

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a Kano yayin wani shiri na karfafa gwiwa da mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibrin ya shirya inda aka raba motoci da babura 1,200 ga shugabannin jam’iyyar.

 

Ya yaba da himmar da gwamnatin ke yi na sake fasalin tattalin arziki yana mai jaddada cewa gyare-gyaren ya taimaka wajen samar da kwanciyar hankali da kuma shimfida hanyar samun ci gaba mai dorewa a Najeriya.

 

“A karkashin jagorancin shugaba Tinubu mun shaida gagarumin ci gaba wajen farfado da tattalin arzikin kasa.

 

“Wadannan yunƙurin sun riga sun samar da sakamako waɗanda suka haɗa da ingantattun ababen more rayuwa da samar da ayyukan yi da bunƙasa a sassa daban-daban.

 

“Raguwar farashin abinci da aka yi a baya-bayan nan da faduwar farashin man fetur da kuma darajar naira duk sakamakon wadannan sauye-sauye ne kai tsaye” in ji shi.

https://x.com/GovUmarGandujee/status/1893784850013806693?ref_src=twsrc%5Etfw%7Ctwcamp%5Etweetembed%7Ctwterm%5E1893784850013806693%7Ctwgr%5E4c147da729e90872d3eb1e700ed5985801e3de19%7Ctwcon%5Es1_&ref_url=https%3A%2F%2Fvon.gov.ng%2Fapc-chairman-praises-president-tinubus-successful-economic-reforms%2F

A cewar shi shugaban ya rike Kano da daraja shi ya sa ya nada su a wasu muhimman mukamai.

 

Sun hada da shugaban jam’iyya mai mulki ta kasa mataimakin shugaban majalisar dattawa ministoci biyu darakta-janar na cibiyar samar da kayayyaki ta kasa da shugaban bankin jinginar gidaje na tarayya da dai sauransu.

 

Gwamna Ganduje ya yabawa Barau bisa kokarinsa na kafa hukumar raya yankin arewa maso yamma tare da godiya ga shugaban kasar shima.

 

Shugaban na kasa ya yi kira ga al’ummar jihar da su marawa gwamnatin Tinubu baya.

 

Ya kuma ce rabon motocin da babura an yi shi ne da nufin inganta rayuwar al’umma musamman ‘yan jam’iyya.

 

Wannan matakin in ji shi ana kuma sa ran zai inganta kyawawan ra’ayoyin jam’iyyar.

 

Tun da farko, Jibrin ya bayyana cewa shirin na da nufin karfafawa ‘ya’yan jam’iyyar APC damar cimma manufofin jam’iyyar.

 

Ya bayyana cewa za a raba baburan ne ga daukacin shugabannin jam’iyyar APC na unguwanni da shugabannin kananan hukumomi na kananan hukumomi 44 na jihar.

 

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya kuma ce nan ba da jimawa ba za a fara wani shiri na musamman na matasa, mata, malamai, dalibai da sauran masu ruwa da tsaki.

 

Ya ce an yi hakan ne domin tabbatar da cewa al’umma sun anfana daga ribar dimokuradiyya.

 

“Muna kuma shirin karfafa wa daliban da suka kammala jami’o’in da ba su samu aiki ba.

 

Ya kara da cewa “Za a zabo wadanda suka kammala digiri uku daga kowace karamar hukuma kuma za su karbi lamuni na Naira miliyan biyar don fara kananan sana’o’i.”

 

Barau ya bayyana cewa salon shugabancin Ganduje ya kara wa jam’iyyar karfi sosai inda ya nuna cewa a karkashin jagorancin shi jam’iyyar ta samu gagarumin ci gaba.

 

Ya kuma yaba wa shugaban kasar kan sauye-sauyen da ya yi na ciyar da kasar gaba.

 

Jibrin ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar da su hada kai domin marawa kokarin shugaban kasa na ciyar da kasa gaba.

 

 

 

Ladan  Nasidi.

 

Comments are closed.