Mutanen Bagwai da Shanono, Sun Gamsu da Barau a Matsayin Dantakar Gwamnan Kano a 2027
Abdulkarim Rabiu
A wani yunkuri na nuna goyan bayan da godiya, wata babbar tawagar wakilai daga kananan hukumomin Bagwai da Shanono na jihar Kano dake arewa maso yammacin Najeriya ta kai ziyarar ban girma ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin. Tawagar, wacce tsohon dan majalisar wakilai Hon. Faruk Lawan ya jagoranta, ta kunshi matasa, da dattawa, da mata daga daukacin mazabar ta tarayya.
An gudanar da ziyarar ne da nufin nuna godiya ga irin tallafin da ba ya misaltuwa da kuma shirye-shiryen inganta rayuwa da dama da suka yi tasiri mai kyau da Sanata Barau Jibrin ke bayarwa ba kawai ga Bagwai da Shanono ba, har ma da dukkan jihar Kano . Tawagar ta yaba da jajircewarsa ga ci gaban jama’a da kuma tsarinsa na tunkarar bukatun jama’ar mazabarsa.
Da yake gabatar da jawabinsa, Hon. Faruk Lawan ya yaba wa Sanata Barau dangane da rawar da ya taka wajen dawo da zaman lafiya, da kwanciyar hankali a lokacin kalubalen tsaro da suka shafi yankin kwanan nan. Ya nuna dimbin gudunmawar da Sanatan ya bayar, ciki har da gina rijiyoyin burtsatse, da makarantu, da asibitoci, da hanyoyi, da kuma samar da guraben karatu, da damar samun aiki, da kayayyakin abinci, da takin zamani, da ababen hawa, da kuma tallafin kudi kai tsaye ga jama’a.
Tawagar ta amince da Shugaba Bola Tinubu a matsayin Dantakarar Shugaban Kasa a 2027, sannan Sanata Barau Jibrin ya zama dan takarar da suka fi so a zaben Gwamnan Jihar Kano na 2027, inda suka yi alƙawarin bashi cikakken goyon bayansudomin cika burinsa. Sun kuma bayyana goyon bayansu ga Hon. Faruk Lawan a matsayin zaɓinsu na wanda zai wakilci Mazabar Tarayya ta Bagwai da Shanono a babban zaɓen 2027.
A martaninsa, Sanata Barau Jibrin ya nuna matuƙar godiya ga ziyarar da kuma gagarumin goyon bayan. Ya sake jaddada sadaukarwarsa ga yi wa jama’a hidima, yana mai jaddada cewa manufarsa ita ce bunkasa rayuwar jamaa ta hanyar samar da ayyukan ci gaba masu ma’ana. Ya mai tabbatar wa tawagar cewa zai ci gaba da ƙoƙari na inganta tsaro da aiwatar da manufofi waɗanda za su amfanar da jama’ar Jihar Kano kai tsaye.
Ziyarar ta ƙare da babban matsayi, wanda ke nuna sabuwar alaƙa tsakanin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa da mutanen Bagwai da Shanono, da kuma hangen nesa na samun ci gaba a Jihar Kano.
Abdulkarim Rabiu