Hukumar hada-hadar kudi ta Afirka (AFC) na kara zage damtse wajen tattara jarin cikin gida don zuba jari tare da neman kudade daga yankin Gabas ta Tsakiya da Asiya yayin da kasashe masu tasowa ke fuskantar sauyin yanayin kudi a duniya.
Samaila Zubairu, Shugaban Hukumar AFC wata cibiyar hada-hadar kudi ta ci gaba mallakin babban bankin Najeriya da wasu kungiyoyin kudi na Afirka ya ce mai ba da lamuni a shirye yake ya zagaya duniyar da taimakon Amurka da Turai ke raguwa.
“Babban canjin da muke son gani shine samar da jarin cikin gida don zuba jari a Afirka” in ji Zubairu. AFC na da niyyar ba da dala biliyan 15-20 daga asusun fensho na Afirka da masu saka hannun jari na hukumomi zuwa ayyukan cikin gida na cikin dogon lokaci.
Karancin kudaden tanadi na Afirka da kasuwannin hada-hadar kudi sun kawo cikas ga kokarin da ake yi na amfani da albarkatun cikin gida. Duk da haka AFC wanda ke tura dala biliyan 2.5- $ 3 a kowace shekara yana taka tsantsan yana haɓaka kudaden da ake kashewa ta hanyar zabar ayyukan da za su iya jawo hankalin masu zuba jari.
Ɗaya daga cikin irin wannan shiri shine InfraCredit, wani shiri na gwaji wanda ke tallafawa saka hannun jarin asusun fensho a cikin ababen more rayuwa wanda aka goyi bayan garantin daga asusun arziƙi na Najeriya. Aikin ya tara naira biliyan 230 (dala miliyan 152) daga asusun fansho guda 21, wadanda a baya suka zuba jari kusan kacal a basussukan gwamnati. Zubairu yana sa ran sake yin irin wannan shirye-shirye a Botswana da Angola da Kenya a farkon wannan shekara.
“Wannan shine irin shirin da muke bukata don haɓakawa” in ji shi.
“Tare da ƙarin shirye-shirye irin wannan za mu iya buɗe biliyoyin don saka hannun jari.”
Kudaden fensho na Afirka kuma sun ba da gudummawa ga asusun jure yanayin yanayin more rayuwa tare da alkawarin dala miliyan 52 daga bankin zuba jari na Turai. Masu zuba jari daga yankin Gulf da Turai suna ƙara sha’awar ayyukan da AFC ke jagoranta kamar Dandamalin ARISE Integrated nda ke ba da kuɗi da haɓaka ayyukan masana’antu.
A halin da ake ciki manufar Shugaban Amurka Donald Trump na “Amurka ta Farko” da kuma rage tallafin da ake ba wa ketare na barazanar fitar da biliyoyin kudi daga ayyukan ci gaban Afirka. Haka kuma kasashen Turai na sauya wasu muhimman batutuwan da suka shafi bayar da agaji inda Birtaniyya ke karkata kudaden zuwa kudaden da ake kashewa na tsaro.
Har yanzu Washington ba ta bayyana shirinta na saka hannun jari ba kan hanyar Lobito Corridor aikin layin dogo da zai hada Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango mai arzikin albarkatun kasa da Zambia da tashar ruwan Lobito ta Atlantic ta Angola.
Reuters/Ladan Nasidi.