Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Kafa Hukumomin Yanki Tare Da Mika Sunanyensu Ga Majalisar Dattawa

60

Shugaban kasa Bola Tinubu ya mikawa majalisar dattawa jerin sunayen wadanda aka zaba na sabbin Hukumomin ci gaban Arewa ta tsakiya da Kudu maso Yamma da Kundu inda ya nemi a tantance su.

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ne ya karanta jerin sunayen a ka’ida a Red Chamber wanda ke nuni da cewa an fara aiwatar da dokar kafa kwamitocin hukumomin shiga tsakani na yankin.

Shagaban kasa Tinubu ne ya ba
Sanata Olubunmi Adetunbi daga jihar Ekiti a matsayin shugaban hukumar raya Kudu maso Yamma tare da wasu mutane 17 inda Dr. Charles Akinola ne zai zama Manaja Daraktan.

Hukumar raya yankin Arewa ta tsakiya tana da mutane 19 da aka nada tare da Cosmas Akiyir da Cyril Yeltsin wadanda aka gabatar a matsayin shugaba da Manajan Darakta.

An aika da jerin sunayen ga kwamitocin da suka dace na Majalisar Dattawa inda Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya umarce su da su gabatar da rahotonsu nan da makonni biyu.

Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.