Take a fresh look at your lifestyle.

Hajj 2025: VP Shettima Ya Bude Jirgin Alhazai Na Farko

150

A ranar Juma’a da ta gabata ne mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya kaddamar da jirgin farko na maniyyatan a Najeriya don gudanar da aikin Hajjin na 2025 a filin jirgin sama na Sam Mbakwe International Cargo Airport Owerri da ke jihar Imo.

Taron dai shi ne na farko da ya fara tashi daga filin jirgin sama na Jihar Imo inda mahajjata 315 daga Imo da Abia da Bayelsa za su tashi a jirgin Air Peace zuwa Saudiyya.

Mataimakin Shagaban kasa Shettima ya samu karba daga Gwamna Hope Uzodinma na Imo da Shugaban Hukumar Alhazai na Najeriya (NAHCON) Farfesa Abdullahi Usman da Sarkin Musulmi Mai Martaba Alhaji Muhammadu Sa’adu Abubakar III da sauran manyan jami’an gwamnati.

Akalla mahajjatan Najeriya 43,000 ne da suka yi rajista ta Jihohi 36 na Najeriya da babban birnin tarayya Abuja za su bi sahun takwarorinsu na Musulmi daga sassan duniya domin gudanar da aikin Hajjin bana.

Shugaban Hukumar NAHCON ya bayyana shirin hukumar na samar da ayyukan Hajji na shekarar 2025 ba tare da wata matsala ba ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki da su kasance da hadin kai da jajircewa wajen samar da ingantacciyar ayyuka ga maniyyatan.

“Ina tabbatar wa duk masu ruwa da tsaki cewa NAHCON ta himmatu wajen samar da hadin gwiwa mai karfi da hada kai don tabbatar da nasarar ayyukan Hajji na 2025.”

Har ila yau kwamishinan ayyuka na NAHCON Alhaji Anofi Elegushi ya jaddada kudirin hukumar na inganta ayyukanta.

An baiwa Air Peace aikin hajji 5,128 daga Abia da Akwa Ibom da Anambra da kuma Sojoji da Bayelsa Benue Borno Cross River da Delta Ebonyi Edo Ekiti Enugu Imo Kogi Ondo Ribas da Taraba.

Hukumar ta FlyNas dai ta ware ma alhazai 12,506 ne daga babban birnin tarayya Kebbi Lagos Ogun Osun Sokoto da Zamfara.

Kamfanin Max Air yana jigilar maniyyatan da suka fito daga jihohin Bauchi Gombe Jigawa Kano Katsina Kwara Oyo da Plateau tare da alkawarin kammala jigilar maniyyatan 15,203 nan da ranar 24 ga watan Mayu.

Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.