Take a fresh look at your lifestyle.

Sanatocin Uku Daga Kebbi Sun Gana Da Shugaba Tinubu

46

Sanatocin jihar Kebbi uku ne suka gana da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu inda suka bayyana aniyarsu na komawa jam’iyyar APC.

Sanatocin da suka kasance jiga-jigan babbar jam’iyyar adawa People’s Democratic Party PDP; Sanata Adamu Aliero mai wakiltar Kebbi ta tsakiya Sanata Yahaya Abubakar Abdullahi mai wakiltar Kebbi ta Arewa da kuma Sanata Garba Maidoki mai wakiltar mazabar Kebbi ta Kudu duk an kai su ofishin shugaban kasa a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Juma’a da ta gabata.

Sanatocin sun samu rakiyar Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki kasa Atiku Bagudu da Gwamnan Jihar Kebbi Mohammed Nasir Idris da Kuma Gwamnan Jihar Sakkwato Ahmad Aliyu Sokoto da sauran jiga-jigan jam’iyyar APC na jihar Kebbi.

Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.