‘Yan majalisar dokokin Najeriya sun yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2023 a kan lokaci.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Lawan, yayin da yake yabawa shugaban kasar ya kara da cewa har yanzu tattalin arzikin Najeriya na fuskantar kalubalantar karancin kudaden shiga, kasancewar babbar hanyar samun kudaden shiga ga gwamnatin Najeriya ita ce mai da iskar gas.
“Babban satar mai da aka yi mana, ya shafi haka ne, saboda hakan yana rage yawan kudaden shiga da gwamnati ke samu,” in ji shi.
A nata bangaren, Sanata Uche Ekumife, ta bayyana gabatar da kasafin a matsayin mai girma.
Sai dai ta ce shugaban kasa ba zai iya gaya wa ‘yan majalisar cewa kada su taba kasafin kudin ba saboda “mu ba ‘yan majalisa ba ne masu tambarin roba”.
Shugaban Majalisar Wakilai, Honarabul Femi Gbajabiamila, ya ce dole ne a sanya kasafin kudin ya yi wa jama’a aiki. Sai dai ya shawarci gwamnati da ta dakile masu satar man fetur yayin da suke zagon kasa ga tattalin arzikin Najeriya.
Hon. Bashir Bichi, yace majalisar dattijai za ta yi kokarin ganin ta gaggauta amincewa da kasafin kudin. Ya ce kasancewar kasafin na karshe na gwamnatin Buhari, akwai bukatar a tabbatar da cewa ta kammala mafi yawan ayyukan gwamnatin.
Hakazalika, Honarabul Benjamin Kalu ya ce za a bi diddigin yadda hukumomin gwamnati ke kare kasafin kudin. Ya ce majalisar za ta kara zage damtse wajen ganin dukkanin hukumomin gwamnati sun zo domin kare kasafin su ba tare da uzuri ba.
Leave a Reply