Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisar Dattawa Don Kasafin Kudi FCT A 2025.

104

Shugaban kasa Bola Tinubu ya nemi amincewar majalisar dattawan kasar don amincewa da kudurin kasafin kudin gwamnatin tarayya na shekarar 2025.

An ruwaito cewa bukatar ta shugaba Tinubu na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aike wa shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio kuma aka karanta a zauren majalisa ranar Laraba da ta gabata

“A bisa ga sashe na 299 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya da aka yi wa kwaskwarima wanda ya bai wa majalisar dokokin tarayya ikon mallakar babban birnin tarayya.

A nan na gabatar da kudirin kasafin kudin FCT na 2025 ga Majalisar Dattawa domin tantancewa.

“Tsarin Kasafin Kudi na FCT na 2025 ya ba da fifikon saka hannun jari a ayyukan kiwon lafiya samar da ayyukan yi karfafa matasa ayyukan jin dadin jama’a kayayyakin more rayuwa na ilimi tare da kara yawan aiki a aikin gona ” in ji wasikar a wani bangare.

Shugaban ya bayyana cewa kasafin kudin na da nufin fitar da ‘yan kasar da dama daga kangin talauci inda ya kara da cewa an kashe jimillar naira tiriliyan 1.7 na kasafin kudin shekarar 2025.

Ya ce kashi 85 cikin 100 na kudaden da ake kashewa an sadaukar da su ne don kammala ayyukan da ake gudanarwa, yayin da aka ware kashi 15 cikin 100 na sabbin manyan ayyuka.

“Wannan shi ne don ci gaba da kokarin da ake yi na samar da kayayyakin more rayuwa da abubuwan jin dadin jama’a a cikin FCT” in ji shi.

Shugaban ya bayyana fatan cewa kudirin kasafin kudin zai samu gagarumin nazari tare da amincewa da majalisar dattawa.

NAN/Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.