Take a fresh look at your lifestyle.

Masu ruwa da tsaki daga jam’iyyar APC reshen Jihar Legas sun amince da sake zaben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu. Taso daga taron da gwamnan Jihar Babajide Sanwo-olu ya kaddamar, shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress APC mai mulki baki daya day Ke legas sun amince da takarar shugaban kasa karo na biyu. Gwamnan ya ce “duk wanda ke da matsala a Legas ya yarda cewa Shugaba Tinubu ya cancanci wa’adi na biyu.” “Dukkan wakilan masu ruwa da tsaki sun cimma matsaya kan cewa ya kamata shugaba Tinubu ya gabatar da kansa a zauren majalisa domin ya dawo a matsayin shugaban mu,” inji shi. Daga nan ne wani babban basaraken gargajiya a Jihar Oba Kabir Shotobi ya gabatar da kudirin daukar shugaban kasa a matsayin Dan takara daya tilo, sannan kakakin majalisar dokokin Jihar Legas, Mudasiru Obasa ya goyi bayansa. Shotobi ya ce “A madadin sarakunan gargajiya a Legas, ni, Ayangburen na Ikorodu, Oba Kabiru Shotobi, mu a Legas muna goyon bayan Shugaba Tinubu ya sake tsayawa takara a karo na biyu,” in ji Shotobi. Shima da yake jawabi a wajen taron, tsohon gwamnan Legas, Babatunde Raji Fashola, ya yi kira da a samar da tsarin jam’iyyar da zai bai wa matasa ‘ya’yan jam’iyyar dama da kuma rawar da za su taka domin ci gaban jam’iyyar a zabe mai zuwa. Aisha. Yahaya, Lagos

40

 

Masu ruwa da tsaki daga jam’iyyar APC reshen Jihar Legas sun amince da sake zaben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu.

Taso daga taron da gwamnan Jihar Babajide Sanwo-olu ya kaddamar, shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress APC mai mulki baki daya day Ke legas sun amince da takarar shugaban kasa karo na biyu.

Gwamnan ya ce “duk wanda ke da matsala a Legas ya yarda cewa Shugaba Tinubu ya cancanci wa’adi na biyu.”

Dukkan wakilan masu ruwa da tsaki sun cimma matsaya kan cewa ya kamata shugaba Tinubu ya gabatar da kansa a zauren majalisa domin ya dawo a matsayin shugaban mu,” inji shi.

Daga nan ne wani babban basaraken gargajiya a Jihar Oba Kabir Shotobi ya gabatar da kudirin daukar shugaban kasa a matsayin Dan takara daya tilo, sannan kakakin majalisar dokokin Jihar Legas, Mudasiru Obasa ya goyi bayansa.

Shotobi ya ce “A madadin sarakunan gargajiya a Legas, ni, Ayangburen na Ikorodu, Oba Kabiru Shotobi, mu a Legas muna goyon bayan Shugaba Tinubu ya sake tsayawa takara a karo na biyu,” in j

Shima da yake jawabi a wajen taron, tsohon gwamnan Legas, Babatunde Raji Fashola, ya yi kira da a samar da tsarin jam’iyyar da zai bai wa matasa ‘ya’yan jam’iyyar dama da kuma rawar da za su taka domin ci gaban jam’iyyar a zabe mai zuwa.

 

Aisha. Yahaya, Lagos

Comments are closed.