Take a fresh look at your lifestyle.

Wata Hukuma Ta Yaba Da Dabarun Tsaron Shugaba Tinubu

22

Hukumar Zakka da Bayar da Kyauta ta Jihar Sokoto ta yabawa matakin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauka na dakile kalubalen tsaro a kasar nan.

Shugaban Hukumar Muhammad Lawal Maidoki ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka shirya domin bayyana ayyukan tunawa da makon Shaikh Usmanu Bn Fodiyo karo na 12 a Sokoto.

Ya bukaci ‘yan kasar da su ci gaba da yin hadin gwiwa kan nasarorin da aka samu wajen magance matsalolin tsaro ta hanyar tallafa wa gwamnati da bayanan da suka dace da za su taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a fadin NajWataeriya.

Yayin da yake yabawa kokarin gwamnati na tunkarar kalubalen tsaro, Maidoki ya bayyana fatan cewa za a dauki karin matakan da suka dace don dakile matsalar tare da tabbatar da tsaro a duk sassan kasar nan.

Ya kuma yabawa gwamnatin jihar Sokoto karkashin jagorancin gwamna Ahmed Aliyu bisa jajircewarta na tabbatar da tsaro a jihar.

Maidoki ya kuma yabawa Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, inda ya bayyana ta a matsayin wata fitilar zaman lafiya, juriya da zamantakewar al’umma a kasar nan.

Kokarin da mai martaba ya yi da kuma kyakkyawar alaka da masu ruwa da tsaki a harkar samar da zaman lafiya – Musulmi da wadanda ba musulmi ba – don samar da zaman lafiya a Najeriya bai kamata kawai a mutunta shi da kuma yabawa ba, har ma da goyon bayan dukkan ‘yan kasa masu kishi,” in ji shi.

Maidoki ya jajantawa iyalan jaruman da suka sadaukar da rayukansu domin kare kasar, yana mai cewa.

Muna kuma jajantawa ‘yan gudun hijirar (IDPs) da sauran wadanda aka kashe a ayyukan muggan laifuka, musamman ‘yan fashi da makami da garkuwa da mutane, da kuma wadanda bala’o’i ya shafa kamar ambaliyar ruwa da aka fuskanta a sassa daban-daban na kasar.”

A cewar Maidoki, makon Shaikh Usmanu Bn Fodiyo karo na 12, mai taken “Rayuwar Jagorancin Da’a da Zamantakewa: Darussa Daga Shugabannin Sakkwato,” zai gudana ne daga ranar 18 ga Oktoba zuwa 2 ga Nuwamba, 2025.

 

Comments are closed.