Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Kasa Tinubu Ya amince Da Murabus Din Ministan Tsaro Mohammed Badaru

34

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da murabus din ministan tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya sauka daga mukaminsa ba tare da bata lokaci ba, saboda matsalar lafiya.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Mista Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Latina da ta gabata ta bayyana cewa tsohon ministan ya mika takardar murabus dinsa ne a wata wasika mai dauke da kwanan wata 1 ga watan Disamba, wacce ta aikewa shugaban kasar.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, shugaba Tinubu, yayin da yake amincewa da matakin na Badaru, ya nuna jin dadinsa kan hidimar da ya yi wa kasa.

Ana sa ran shugaban kasar zai sanar da maye gurbin Badaru ga majalisar dattawa a cikin wannan mako yayin da ake ci gaba da tuntubar juna.

Badaru Abubakar, mai shekaru 63, ya rike mukamin gwamnan Jihar Jigawa na tsawon wa’adi biyu tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023 kafin a nada shi ministan tsaro a ranar 21 ga watan Agustan 2023.

Ficewar tsoffin ministocin na zuwa ne a daidai lokacin da shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan tsaron kasa, tare da karin bayani kan iyakar manufofin da ake sa ran nan ba da dadewa ba.

 

Aisha. Yahaya, Lagos

 

Comments are closed.