Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yabawa Majalisar Dattawan Najeriya bisa gaggautar amincewa da Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro.
A cikin wani sakon da aka sanya a hannun jami’in sa na X @OfficialABAT Shugaban ya bayyana nadin a matsayin “yana zuwa a wani muhimmin lokaci.”
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa kwanaki biyu kacal ya mika wa majalisar dattijai sunan Janar Musa sannan ya yabawa ‘yan majalisar kan matakin da suka dauka cikin gaggawa wajen ciyar da gwamnatin sa gaba.
Shugaban na Najeriya ya kuma yaba wa tsohon Hafsan Hafsoshin Sojan Najeriya a matsayin “Mutumin Kirki na Gaske” wanda halayen jagoranci da kwarewar aiki za su taimaka wajen karfafa gine-ginen tsaron Najeriya.
“Kwanaki biyu da suka wuce, na mika sunan Janar Christopher G. Musa wato tsohon babban hafsan hafsoshin tsaronmu kuma babban mutum mai daraja ga majalisar dattawan Najeriya domin tabbatar da shi a matsayin ministan tsaro na tarayya.
“Ina so in yaba wa Majalisar Dattawan Najeriya bisa gaggauta tabbatar da Janar Musa a jiya. Nadin nasa ya zo a wani muhimmin lokaci a rayuwarmu ta kasa baki daya.”
Nadin Janar Musa a matsayin Ministan Tsaro ya biyo bayan murabus din da magabacin sa Alhaji Mohammed Badaru Abubakar ya yi a farkon makon nan.