Take a fresh look at your lifestyle.

Tinubu Ya Amince Da Naira Biliyan 47 Na Aikin Titin Kano

37

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kashe zunzurutun kudi har naira biliyan 47 domin kammala aikin titin garin Wuju-Wuju/Jakara mai tsawon kilomita 6.7 da samar da magudanar ruwa a cikin babban birnin jihar Kano.

Karamin ministan gidaje da raya birane, Alhaji Yusuf Abdullahi Ata ne ya bayyana hakan yayin wani karin haske da aka gudanar a Kano.

Ya bayyana shiga tsakani a matsayin wata karara ta nuna jajircewar shugaba Tinubu wajen sabunta birane da samar da ababen more rayuwa, da bunkasar tattalin arziki a jihar.

A cewar Ata “aikin wanda zai raba kananan hukumomi hudu zai yi matukar tasiri ga tattalin arzikin Kano.”

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana son jihar Kano kuma dole ne mu yaba da wannan wannan wani gagarumin aiki ne da gwamnatin Tinubu ta baiwa Kano.

“Saboda hanyar ta yanke kan kananan hukumomi hudu tasirin tattalin arzikinta zai yi yawa.”

Ata ya bayyana cewa amincewar da shugaban kasa ya yi na kudade zai tabbatar da kammala aikin a kan lokaci wanda ya tsaya cik shekaru da dama.

Ya kara da cewa gwamnatin Najeriya ta karbi aikin ne ta hannun ma’aikatar gidaje da raya birane ta tarayya biyo bayan bukatar da gwamnatin jihar Kano ta gabatar a hukumance.

Wannan shiga wani bangare ne na kudurin shugaban kasa na tallafawa jihohi wajen isar da muhimman ababen more rayuwa wadanda ke shafar rayuwar jama’a kai tsaye” in ji Ministan.

Ya kuma bayyana cewa aikin titin da magudanar ruwa ya ratsa ta kananan hukumomin Gwale da Kano Municipal da Dala da Fagge inda ya jaddada cewa kammala aikin zai taimaka matuka wajen saukaka zirga-zirga da inganta tsaftar muhalli da bunkasa harkokin kasuwanci a babban birnin jihar.

Idan aka kammala wannan hanyar zata yi tasiri ga rayuwa da tattalin arzikin mazauna a fadin wadannan kananan hukumomin” in ji Ata.

Ministan ya bayyana cewa yayin da gwamnatin jihar Kano ta kammala kusan mita 850 na hanyar gwamnatin Najeriya zata aiwatar da sauran kilomita 6.7 domin tabbatar da kammala aikin.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ce ke da alhakin biyan diyya ga masu kadarorin da abin ya shafa inda ya ce tuni aka biya diyya mai kusan kilomita biyu.

Da yake tabbatar da isar da inganci Ata ya ce mai kula da gidaje a ma’aikatar gidaje da raya birane ta tarayya ne zai kula da aikin.

Ata ya yabawa gwamnatin tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso bisa kaddamar da aikin a shekarar 2013 tare da ware naira biliyan 5 domin fara aikin, inda ya bayyana matakin da gwamnatin tarayya ta yi a halin yanzu a matsayin ci gaba da wannan hangen nesa na kawo sauyi a biranen Kano.

 

Comments are closed.