Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai bar Abuja ranar Litinin, 26 ga watan Janairu, domin ziyarar aiki a Jamhuriyar Turkiyya.
Ziyarar na da nufin karfafa dankon zumuncin da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma duba wasu fannonin hadin gwiwa a fannonin tsaro, ilimi, ci gaban zamantakewa, kirkire-kirkire, da sufurin jiragen sama.
Wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru, Mista Bayo Onanuga, ya fitar ya bayyana cewa, yayin ziyarar ta shugaba Tinubu, kasashen biyu za su yi tattaunawa ta siyasa da diflomasiyya bisa manyan tsare-tsare a fannonin kudi, sadarwa, kasuwanci, da zuba jari.
Ajandar za ta hada da ganawa tsakanin manyan jami’an kasashen biyu, da kuma rattaba hannu kan yarjejeniyoyin fahimtar juna a bangarori daban-daban, da suka hada da binciken kimiyya, makamashi, hadin gwiwar fasaha, kafofin watsa labaru da sadarwa, hadin gwiwar soja, da yarjejeniya da dai sauransu.
Dandalin Kasuwanci
Taron kasuwanci zai hada masu zuba jari daga kasashen biyu don gano wuraren da za su kayatar yayin ziyarar.
Mambobin tawagar shugaban kasar da ke halartar shawarwarin sun hada da: Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar; Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi SAN; Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (rtd); kuma Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar, Hon. Jimi Benson.
Sauran sun hada da: Ministar harkokin mata da ci gaban zamantakewa, Hajiya Imaan Suleiman-Ibrahim; Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo; Ministar Al’adu da Tattalin Arziki Ƙirƙiri, Hannatu Musawa; Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu; da Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Ambasada Mohammed Mohammed.
Ana sa ran shugaba Tinubu zai dawo gida Abuja a karshen ziyarar.
Ku tuna cewa shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kai ziyarar aiki Najeriya a watan Oktoban 2021.
Aisha. Yahaya, Lagos