Gwamnatin Jihar Nasarawa ta bada wani kalubale ga Kamfanonin Hakar Ma’adanai na kasashen waje da na sana’o’in hannu da su sauke nauyin da yake a kan su na zamantakewar al’umma ta hanyar samar da ayyuka ga al’ummomin da ke hakar ma’adinai.
Kwamishiniyar Muhalli da Albarkatun Kasa ta Jihar, Dakta Margaret Elayo ta bayyana wannan kalubalen a lokacin kaddamar da wasu muhimman ayyuka na al’umma da suka hada da fitulun hasken rana arba’in da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana guda goma da kuma tallafin magunguna na naira miliyan biyu ga cibiyar lafiya matakin farko (PHC) da ke Uke, karamar hukumar Karu, wani shiri da aka yi tare da hadin gwiwar Sawadogo Nig Ltd.
Dokta Elayo ta bayyana damuwar ta kan yadda yawancin kamfanonin hakar ma’adinai, duk da samun lasisin da suka dace da kuma filaye don hakowa, sukan yi watsi da nauyin da ya rataya a wuyansu na zamantakewa.
Wannan sakaci yawanci yana haifar da tashe-tashen hankula da rashin fahimtar juna tsakanin kamfanonin hakar ma’adinai da kuma al’ummomin da ke karbar bakuncin, musamman game da muhimman ayyuka kamar hakar rijiyoyin burtsatse da tallafin karatu na ilimi ga ɗalibai da wuraren kiwon lafiya.
Ta ce kamfanin Sawadogo Nig Enterprises Ltd da ke aiki a Uke, ya kafa misali mai kyau ta hanyar bin ayyukan da ya rataya a wuyan su, wanda hakan ya nuna ta hanyar bayar da tallafin magunguna na naira miliyan biyu ga hukumar ta PHC da samar da fitulun hasken rana arba’in da hakar rijiyoyin burtsatse guda goma ga al’umma.
A yayin kaddamar da aikin Dr. Elayo ya bayyana cewa dole ne kamfanonin hakar ma’adinai su bada gudummawa mai kyau ga rayuwar al’ummomin da ke karbar bakuncin.
“Duk lokacin da kuke jihar Nasarawa kuma kuna son yin ayyukan hakar ma’adinai, muna bukatar ku yi abin da ya dace don kauce wa matsaloli da samar da kudaden shiga da ya kunshi ayyuka sannan kuma dole ne ku bada gudummawar ku ga tsarin,” in ji ta.
Kwamishinan ta yabawa Sawadogo Nig Enterprises Ltd bisa fara ayyukan da suka shafi al’umma wadanda suka dace da shawarwarin ma’aikatar.
“Abin da Sawadogo Nig Enterprises Ltd ya yi wa Uke abin yabawa ne kuma ba na magana ko zuwa wuraren hakar ma’adinai ba tare da fahimtar halin da ake ciki ba; Sawadogo sun bi hanyoyin da suka dace kuma sun biya kudaden su ga gwamnatocin jihohi da na tarayya, shi ya sa suke jin dadin goyon bayanmu.”
Bugu da kari, Dr. Elayo ya lura cewa gwamnatin jihar ta himmatu wajen sa ido kan yadda kamfanonin hakar ma’adinai ke bin ka’idojin CSR kuma tana samar da wani tsari na tabbatar da bin ka’ida.
Ta kara da cewa “Muna tsara manufofin da za su jagoranci da kuma tallafawa kamfanonin hakar ma’adinai a kokarinsu na bayar da gudummawa mai kyau ga al’ummomin da suke aiki a ciki,” in ji ta.
Da yake mayar da martani, shugaban kamfanin na Sawadogo Nig Enterprises Ltd, Alhaji Yakubu Sawadogo ya bayyana jin dadinsa ga gwamnatin jihar bisa sabon alkawari da goyon bayan da suke baiwa kamfanin, yayin da ya tabbatar da cewa kamfanin zai bi duk ka’idojin hakar ma’adinai da kuma tasiri ga rayuwar al’ummar da ke aikin hakar ma’adinai.
Bayan kaddamar da aikin, Dakta Margaret ta ziyarci wurin hakar ma’adinai na Sawadogo Nig Enterprises Ltd, inda ta jaddada mahimmancin dorewar muhalli da kuma bukatuwar kwato filaye bayan hakowa.
A yayin ziyarar da ta kai birnin Uke, Dakta Margaret ta ziyarci fadar Yakanajen Uke, domin sanar da mai martaba sarkin yankin inda mai martaba Alhaji Ahmed Abdullahi Hassan, Yakanajen Uke, ya yabawa kwazon kwamishinonin wajen sauke nauyin da aka dora mata.
Ya karrama ta da lakabin gargajiya na Tozalin Uke, kuma ya ba ta tabbacin cewa zai yi amfani da karfinsa wajen tallafa wa kamfanonin hakar ma’adanai da ke aiki a yankinsa.