Naira Biliyan 1.4: Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Kama Dan Takarar Majalisar Dokokin Jihar Kogi
Usman Lawal Saulawa
Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa ta Najeriya, EFCC, ta kama dan takarar majalisar dokokin jihar Kogi a karkashin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Ismaila Yusuf Atumeyi da kudi naira miliyan 326 da kuma Dala dubu dari hudu da arbain da dari biyar ($140,500).
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Mista Wilson Uwujaren ya fitar ta ce, an kama Atumeyi wanda ke neman wakiltar mazabar Ankpa 2 a majalisar dokokin jihar Kogi a ranar Lahadi, 30 ga watan Oktoba, 2022 tare da wani Joshua Dominic, wanda ake zargi da damfara a wani da suka yi a Macedonia Street, Queens Estate, Karsana, Gwarinpa, Abuja.
Har ila yau, an kama wani tsohon ma’aikacin banki, Abdumalik Salau Femi, wanda ake zargin ya bayar da bayanan da suka taimaka wajen kai hari bankin da kungiyar ta yi.
” An tsince shi a yau, 1 ga watan Nuwamba, 2022 a Otal din Radisson Blu da ke Legas. Bayan kama shi, an gudanar da bincike a gidansa da ke Morgan Estate, Ojodu inda aka samu dala $470,000.”
Sanarwar ta ce, kama wadanda ake zargin ya biyo bayan gudanar da bincike na tsawon watanni da wasu ‘yan damfara suka yi wa daya daga cikin bankunan kasuwanci, inda suka zaro makudan kudade da suka kai Naira biliyan 1.4.
Ana zargin kungiyar ta tura Naira miliyan 887 a cikin asusun Fav Oil and Gas Limited, inda aka biya kudaden ga wasu ma’aikatan ofishin canji da wasu dillalan motoci domin yin musaya da dalar Amurka da kuma sayen manyan motoci
“Dominic, wanda aka kama da laifin zamba, ana zargin ya taimaka wa Atumeyi ya kammala shirin kutse ta hannun Abdumalik. Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama Dominic, wani mai kiran kansa kwararre kan harkokin zuba jari kuma manajan darakta na Brisk Capital Limited a watan Mayun 2021 a hannun Sashin damfara na ‘yan sandan Najeriya bisa zargin badakalar zuba jarin N2billion. Ana zarginsa da damfarar sama da mutane 500 a wani shirin saka hannun jari na banza”.
An kuma samu nasarar kwato motoci biyu kirar Range Rover Luxury SUV daga hannun mutanen biyu da aka kama a Abuja. Sanarwar ta kara da cewa, za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike. A halin da ake ciki kuma, hukumar ta nuna damuwarta kan yadda ake samun karuwar hare-haren ta hanyar yanar gizo a bankuna da kuma yadda hukumomin ke nuna rashin amincewa da irin wannan aika-aikar ga jami’an tsaro.
Yayin da take gargadin cewa irin wannan abu ba zai karawa masu laifi kwarin guiwa ba, EFCC ta yi kira ga hukumomin kudi da su hada kai da ita domin kare harkar hada-hadar kudi daga barazanar kai hare-hare ta yanar gizo.
Idan dai za a iya tunawa, hukumar EFCC ta yi gargadin cewa babban bankin Najeriya CBN ya sanar da shirin sake fasalin kasa da kuma sake fitar da wasu manyan darajar Naira, ya gargadi masu gudanar da harkokin canji da su yi hattara da masu satar kudaden da za su yi yunkurin kwace kudaden da suka jibge ba bisa ka’ida ba.
Leave a Reply