A wani taron masu ruwa da tsaki akan harkar tsaro a Maiduguri dake jihar Barno a Arewa maso gabashin Najeriya.
Gwamnan Jihar Farfesa Babagana Zulum,yace: ‘’A bune wanda ya zama wajibi a agazawa karatun Yara Marayu wadanda Iyayensu suka sadaukar da kawunansu wajen kare rayuka da dukiyoyin alummarsu, kamar yadda kuka
Sanina ne gamayyar Kungiyoyin sa Kai wato Sibiliyan JTF, da na Maharbag ami kuma da Vigilantes sun taka rawar gani wajen zakulo su ‘Yan ta’addan a irin halin da muka shiga na Yakin Boko Haram da ya haura shekaru goma , akan haka ne akayi asarar rayuka sun kuma bar Iyalansu da Yaransu,saboda haka muka fahimci cewar bai kamata a bar Yaran hanan suna gararanba a kan Tituna ba. Yanzu zamu dauki nauyin karatun Yaran su Dari 3, akan kudi Naira Miliyan Dari 3.’’
‘’Kuma zamu karawa CJTF yawan Alawus-alwus daga watan gobe, daga yawan Naira Dubu 20, ya zuwa Dubu 30, kana kuma zamu baku kudin
Garabasa wato (Bonus) a wannan karshen shekaran, domin muna fatan su
ci gaba da agazawa Jami’an tsaro wajen zakulo wadannan ‘Yan ta’addan
don magancesu kasancewar sune suka san lunguna da sakuna na wannan
jihar to kuma duk fatanmune wannan abin ya kawo karshe a wannan
lokacin.’’inji Gwamna Zulum
A jawabinsa Bubban Kwamandan Yaki da Boko Haram ta Opration Hadin Kai Manjo Janar Christoper Musa, ya nuna irin kokarin da ‘Yan Kungiyar Sa
Kai ta CJTF, da Maharba gami kuma da Viglantes, ya ce ‘’Babu ko shakka
sun bamu gagarumin hadin kai da goyon baya wajen yaki da wadannan ‘Yan ta’adda kasancewar sun sansu a fuska kuma tare muka shiga Kungurmin Jeji mu Yaki wadannan Mutanen gaba gadi, in da ananne wasu ke rasa rayukansu, to kuma abune mai kyau idan har yau ance Hukumomi suna tallafawa Iyalansu da suka mutu suka barsu.’’
Ya ce ‘’To kuma a irin wannan taimakon da sukeyi manane a yanzu haka
akwai Mayakan Boko Haram da suka mika wuya ga mu Dakarun Najeriya har su sama da Dubu 81, Matansu da Mazajensu, gami kuma da wadanda muka kubutar daga hannun wadannan miyagun mutane.’’
A jawabinsa na godiya Shugaban Kungiyar ‘Yan Sa Kai ta CJTF Ba’Lawan Jafar,yace, ya nuna farin cikin shi dangane da abin da gwamnatin jihar Borno take yi masu musanman daukar nauyin karatun Marayu da kuma kara yawan Alawus,Yace :’’Wannan abun fari cikine ainun kuma muna godewa gwamnti wannan zai taimakawa rayuwar Yaran ta wajen bunkasa harkokin rayuwartasu Allah ya saka da Alkhairi.’’
Tuni Shugaban Kwamitin bayar da Guraben Karatun Barista Kaka Shehu
Lawan, ya tantance Yaran aka amince da Yara Mata har 110, a yayin da Maza suka kasance 190.
Leave a Reply