Take a fresh look at your lifestyle.

Jan Hankali

0 130

An jawo hankalin Hukumar Kula da Muryar Najeriya (VON), zuwa wani shafin yanar gizon JABU: https://voiceofnigeria.org.ng, wanda ake zargin na Muryar Najeriya ne, wanda Cloudflare Inc ya shirya, ba gidan yanar gizon Muryar Najeriya ba ne.

 

 

Don haka muna ba da shawara ga jama’a da su yi watsi da yanar gizon da kuma bayanan da ke cikinsa.

 

 

Sunan da ake amfani da shi wajen rajistar gidan yanar gizon bogi shine .org.ng, wanda ke nuni da cewa ba na gwamnatin tarayyar Najeriya ba ne.

 

Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa, NITDA ta amince da sunan yanar GiZom Muryar Najeriya shine: https://www.von.gov.ng

 

 

.gov.ng shine sunan gwamnatin tarayya da aka amince da shi wanda mafi yawan Ma’aikatu, da Hukumomi kamar VON suka ɗauka.

 

Har yanzu, Voice of Nigeria ba ita ce mai https://voiceofnigeria.org.ng ba kuma ba yanar gizon mu ba ne.

 

Adireshin gidan yanar gizon Muryar Najeriya shine: https://www.von.gov.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *