Shugabannin kasashen Afirka ta Kudu da na Kenya sun fada jiya Laraba cewa, sun sasanta Tsakanin Su game da visa da aka dade ana yi, kuma ‘yan kasar Kenya za su iya ziyartar Afirka ta Kudu ba tare da biza ba har na tsawon kwanaki 90 a cikin shekara guda.
Tuni dai ‘yan Afirka ta Kudu ke samun biza kyauta idan suka isa Kenya, yayin da ake tuhumar ‘yan Kenya da kuma bayar da shaidar isassun kudade da tikitin dawowar jirgi.
Sabuwar yarjejeniyar dai za ta fara aiki ne a ranar 1 ga watan Janairu.
Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya kai ziyara kasar Kenya a ziyararsa ta farko a hukumance.
Shi da shugaban kasar Kenya William Ruto sun yaba da yarjejeniyar zaman lafiya da kasar Habasha ta kulla a makon da ya gabata a kasar Afirka ta Kudu, wadda kuma kungiyar Tarayyar Afirka ta shiga tsakani.
Sun yi kira ga bangarorin da su “tabbatar da cikakken aiwatar da yarjejeniyar don cimma matsaya ta siyasa mai dorewa.”
Shugabannin kasashen Kenya da na Afirka ta Kudu sun kuma umarci ministocin kasuwancinsu da su magance matsalolin da ke takaita kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
Kasashen biyu na daga cikin kasashe masu karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka.
Leave a Reply