Take a fresh look at your lifestyle.

An Sake Bude Filin Jiragen Sama Na Tanzaniya Bayan Hatsari An sake bude filin tashi da saukar jiragen sama na Bukoba da ke arewa maso yammacin kasar Tanzaniya bayan rufe shi sakamakon wani hatsarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 19. Jirgin fasinja ya fada cikin tafkin Victoria a lokacin da yake kokarin sauka a filin jirgin a ranar Lahadi. Wani ma’aikacin yankin ya ce ana sa ran jirgin farko na fasinja zai sauka a filin jirgin ranar Alhamis. A halin da ake ciki, masu ba da shawara kan fasaha daga kamfanin kera jiragen, ATR, sun kaddamar da bincike kan hadarin. An kuma aike da kwararru kan binciken lafiyar jiragen na Faransa zuwa kasar. Kamfanin Precision Air ne ke sarrafa jirgin, babban jirgin fasinja na Tanzaniya mai zaman kansa. Wanda ke aiki a hanyar Darussalam-Bukoba tun 1994.

Aisha Yahaya

0 300

An sake bude filin tashi da saukar jiragen sama na Bukoba da ke arewa maso yammacin kasar Tanzaniya bayan rufe shi sakamakon wani hatsarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 19.

 

 

Jirgin fasinja ya fada cikin tafkin Victoria a lokacin da yake kokarin sauka a filin jirgin a ranar Lahadi. Wani ma’aikacin yankin ya ce ana sa ran jirgin farko na fasinja zai sauka a filin jirgin ranar Alhamis.

 

 

A halin da ake ciki, masu ba da shawara kan fasaha daga kamfanin kera jiragen, ATR, sun kaddamar da bincike kan hadarin.

 

 

An kuma aike da kwararru kan binciken lafiyar jiragen na Faransa zuwa kasar. Kamfanin Precision Air ne ke sarrafa jirgin, babban jirgin fasinja na Tanzaniya mai zaman kansa. Wanda ke aiki a hanyar Darussalam-Bukoba tun 1994.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *