Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya dawo Abuja daga kasar Ingila inda ya je duba lafiyarsa.
Shugaban Buhari wanda ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja a yammacin jiya Lahadi, ya samu tarba daga shugaban ma’aikatan fadar sa Farfesa, Ibrahim Gambari da ministan babban birnin tarayya Mohammed Bello da babban sufeton janar na fadar gwamnatin tarayya. ‘Yan sanda, Usman Alkali, da dai sauransu.
Shugaba Buhari ya tashi daga gabar tekun Najeriya ne a ranar Litinin 31 ga watan Oktoba, bayan ya halarci taron tsaro na manyan jami’an ‘yan sanda a Owerri, babban birnin jihar Imo.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa Najeriya ya gana da Sarki Charles a Birtaniya . A zamansa na makonni biyu a Burtaniya, shugaban ya kai ziyarar ban girma ga Sarki Charles wanda shi ne ganawarsa ta farko tun hawan Sarkin.

Leave a Reply