Ma’aikatar lafiya ta kasar Masar ta sanar da cewa, mutane 19 ne suka mutu, wasu 6 kuma suka samu raunuka, a lokacin da wata motar bas ta fada cikin mazarari a arewacin Masar a ranar Asabar.
Motar dai na dauke da mutane kusan 35 ne a lokacin da “ta bi ta kan wata babbar hanya ta fada cikin mazarari ta Mansuriya da ke garin Aga,” a cikin lardin Daqahlia da ke arewacin kasar, a cewar majiyoyin tsaro.
Leave a Reply