Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya mamaye jihar Ebonyi dake kudu maso gabashin Najeriya, da yakin neman zaben shi na shugaban kasa.
Tinubu da isowarsa a ranar Laraba, 23 ga watan Nuwamba, 2022 gabanin yakin neman zabe a ranar Alhamis ya kaddamar da sabuwar hanyar mota ta gidan gwamnati a Ochoudo Centenary City, Abakaliki, babban birnin jihar.
Tinubu ya ce ya yi farin ciki da zuwan sa jihar Ebonyi wanda a cewar sa, kamar Dubai.
Yayin kaddamar da aikin, Tinubu ya tabbatarwa dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC Mista Francis Nwifuru cewa za su yi aiki tare domin ganin an samu nasara a babban zabe mai zuwa.
Ya godewa Gwamnan jihar Engr. David Umahi, saboda ci gaban da ya nuna a jihar.
Tinubu ya bayyana Umahi a matsayin jagora wanda ya gina wasu shugabanni.
A nasa bangaren, Gwamna Umahi ya ce an gina sabon katafaren gidan gwamnati ne domin baiwa ma’aikatan jihar damar samun ingantaccen wurin aiki.
Umahi ya godewa dan takarar shugaban kasa da ya sauka a jihar Ebonyi domin jama’a su ji kasancewar dan takarar da suka zaba.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya kuma gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar.
Leave a Reply