Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin jihar Katsina ta kaddamar da wani shiri domin bunkasa noma a jihar

Kamilu Lawal

0 170

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bude wasu wuraren noman rani a yankunan karamar hukumar Matazu da Dutsinma dake jihar

 

 

Wurararen wadanda aka bude lokacin wani taro da ya gudana a cibiyar nazarin dabarun aikin gona ta Songhai dake garin Dutsinma sun kunshi wurin noman rani na Raddawa a karamar hukumar Matazu da na Makera a karamar hukumar Dutsinma

 

 

An samar da wuraren ne sakamakon hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Katsina da gidauniyar Saemaul ta kasar Korea ta kudu tare da tallafin kamfanin Dangote domin bunkasa aikin gona

 

 

Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da wuraren, gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bukaci wadanda da aka saka a cikin shirin da su fadada horon da suka samu ga sauran manoma da makwabtan su bisa la’akari da alfanun dake tattare da harkar ga cigaban al’ummar jihar da kasa baki daya

 

 

Yana mai cewa maida hankali wajen batutuwan da suka shafi juba jari musamman a bangaren noma zai taimaka wajen karfafa tattalin arzikin jihar da kasa baki daya

 

 

Ya yaba da kokarin da Alhaji Aliko Dangote bisa samar da hadin gwiwar mai matukar tasiri wajen bada gudummuwar ayyukan noma da tattalin arziki a jihar

 

 

Da yake nasa jawabin babban darektan hukumar bunkasa saka jari ta jihar Katsina(KIFA) Ibrahim Tukur Jikamshi yace wuraren noman ranin guda biyu na daga cikin nasararorin da hukumar ta samu a shirinta na fadada zuba jari a jihar

 

 

Yana mai cewa bude wadannan wurare wani bangare ne daga cikin nasarorin da shirin ya samu a jihar

 

 

A jawabin sa a wajen taron, shugaban gidauniyar ta Saemaul dake kasar Korea ta Kudu Mr,Lee Seung Jong ya bayyana cewa  gidauniyar tazo najeriya ne ta hanyar kamfanin Dangote domin bada gudummuwa wajen bunkasa harkokin noma

 

 

Yace cibiyoyin na Makera da Raddawa da aka zaba domin gudanar da noman daidai da zamani na da nufin bunkasa aikin gonar domin bunkasar tattalin arziki

 

 

 

Tun farko, Ana sa jawabin darektan harkokin gidauniyar Saemaul a najeriya Mr,Kyonbok Lee yace an samar da rijiyoyin burtsatse da dakin ajiye kayayyaki da na gudanar da taro da sauran bukatu a wuraren noman domin cimma nasarar shirin a jihar Katsina

 

 

Shima wakilin Dangote a wajen taron Injiniya Mansir ya godema gwamnatin jihar bisa damar da ta bada ga shirin tare da fatan gudummuwar da suka bayar zata samar da nasarar da ake bukata

 

 

Sama dai hecta d’ari ta filin noma ce dai  ake sa ran nomawa kalkashin shirin noman shinkafar a zamanance, al’amarin da ake fatan zai inganta harkar noman tare da samar da aikin yi domin bunkasar tattalin arzikin jihar da kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *