An gudana da bukin baje kolin kirkire-kirkire da Zane-Zane na Zamani, KILAF a Kano Dake Arewa Maso Yammacin Najeriya.
Kasashe daga Afirka suka samu halarta domin musayar raayoyi akan sarrafa fasahar kirkira da Zane da kiyaye Al’adun kasashen Afirka,ta yadda masu shirya fina-finai asu kiyaye anfani da irin fasahar da Allah ya basu wajen gudanar da aiyyukan su a wannan fanni.
Hajiya Khaltum Bulama Gana Jamiar kula da Zane-Zane da kirkire-kirkire na amani a cibiyar kula da fasahar ane da al’adun gargajiya ta Najeriya, tayi bayanin makasudin uwan su wannan babban baje koli na KILAF tace,
“muno wannan babbanbukin baje kolin abubuwa na kirkire –kirkire da mutanen mu keyi da fasahar da suke yi da hannuwan su da kwakwalwar su’’
Game da sauran bakin da suka gayyato,Hajiya Khaltun tace sun gayyato makarantu rubutun Kur’ani da Ajami da sukeyi na Zayyana akan fata da Allo da aduo’I da ake sanya wa a gidaje.
Tace shi wannan rubutun Magaribi kanshi sun bude makarantar yin shi da ke cikin Kano kuma ana karfafa musu kwarin gwuiwa.
Hajiya Khaltun tace; “makasudin kafa wannan makaranta shine domin karfafawa hafiai kwarin gwuiwa na ganin Najeriya ta samu karbuwa tare da gogayya da sauran kasashe dake anfani da ire-iren wannan baiwar’’
HakaZalika Khaltun ta kara da cewa sun gayyaci kungiyar masu Zane-Zane ta Najeriya,musamman kwararru akan wannan harkar.
Babban taron baje kolin KILAF ya samu halartar masu Zane-Zane da shirya fina-finai daga Janhuriyar Nijar da Kenya domin ganewa idanuwan su irin baiwar ‘yan Najeriya.
Zarah Umaru na daya daga cikin tawagar Ministan al’adun su a Nijar ta nuna farin cikin ta na samun halartar wannan baje kolin KILAF na ci gaban shirya fina-finai a harshen Harsunan Afirka a Najeriya,tace.
“tunda makaZo wannan buki a Najeriya akayi mana kyakyawar tarba,mun kuma gana da muhimman kwararru a fannin shirya fina –finai kuma an bamu horo mai kyau a duk bangaren da amu sani a da ba.
“mun samu akan matsalolin dake damun mu wato wajen kasuwancin fina-finan da furodusoshi ke yi a Nijar,Alhamdu Lillah”, in ji Zara
A matsayin ta na Jarumar Fina –finai Kuma mawakiya ta yi fina-finai irin su, “Mahaukacin Masoyi da sauran masu tsawon Zango”,tace bayan sun koma Nijar,ata ci gaba da anfani da koya wa sauran ‘yan uwaabokan aiki ilimin da ta samo daga bukin KILAF.
Bukin naje kolin KILAF dai dandali ne dake bada kwarin gwuiwa da ci gab da shirya fina –finai a cikin harsunan Afirka na asali,da nufin kiyaye wa al’adu da al-adun Nahiyar Afirka tare da tabbatar da cewa ‘yan Afirka suna yada irin wannan manufa ta anfani da harsuna.
KAI wannan bukin ya kayatar kuma mun anfana daga Shi,fatan mu shine sauran kasashen Afirka Suyi koyi da yadda Najeriya ta shirya baje kolin