Babban Lauyan Angola, Helder Groz ya tabbatar da cewa kasarsa ta bayar da sammacin kamo diyar tsohon shugaban kasar Jose Eduardo dos Santos, Isabel dos Santos.
Mista Groz ya ce hukumomin Angola suna aiki tare da Interpol don gano Ms. Dos Santos.
Rahoton ya ce hukumomin Angola sun tuhume ta da laifin almundahana da dukiyar al’umma a lokacin da ta jagoranci kamfanin mai na kasar, Sonangol.
Gwamnati ta shigar da kararraki da dama na farar hula da na laifuka tana neman sama da dala biliyan 5 daga gare ta. Madam Dos Santos ta musanta zargin.
A halin da ake ciki, a cikin wata hira, ta ce tana nan don amsa tambayoyi.
“An san adireshina, an san inda nake,” in ji ta.
“Ni ba mai gudu ba ne. Ba na boyewa kowa,” ta kara da cewa tana zaune a Landan.
Ta kuma bayyana zargin da alaka da siyasa.
Leave a Reply