Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar zartarwa ta tarayya, wanda aka gudanar a dakin taro na fadar shugaban kasa, Abuja.
Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folashade Yemi-Esan na daga cikin wadanda suka halarci taron.
Sauran sun hada da ministocin yada labarai, Lai Mohammed, kudi, kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Zainab Ahmed da Justice Abubakar Malami da dai sauransu.
A dai dai lokacin da majalisar ta fara zaman tattaunawa na ranar, majalisar ta yi shiru na minti daya domin karrama tsohon ministan wutar lantarki da karafa na Najeriya, Paul Unongo, wanda ya rasu a ranar Talata 29 ga watan Nuwamba yana da shekaru 87 a duniya.
Har ya zuwa rasuwarsa, Marigayi Unongo shi ne Shugaban Majalisar Gudanarwa ta Majalisar Cigaban Ilimi ta Najeriya.
Leave a Reply