Kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar APC na Mata a shiyyar arewa maso yamma ya kaddamar da yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da mataimakin sa Khashim Shattima a jihar Katsina arewa maso yammacin najeriya
Taron gangamin wanda ya tattara dubun dubatar Mata magoya bayan jam’iyyar daga jihohin dake shiyyar arewa maso yamma ya gudana ne a dandalin taro na People’s square dake birnin Katsina
Da take jawabi a wajen taron, uwar gidan dan takarar shugaban kasar kalkashin jam’iyyar APC sanata Remi Tinubu ta bayyanawa dandazon matan cewa ita da matar dan takarar mataimakin shugaban kasar Hajiya Nana Shettima sun dauki alkawalin cigaba da inganta rayuwar mata da matasan najeriya idan jam’iyyar ta sake darewa mulkin najeriya
Ta yaba da irin goyon da ta samu daga matan yankin a gangamin yakin neman zaben, tana mai bada tabbacin tabbatar da tallafawa mijinta wajen yin dukkanin mai yiyuwa domin maido da zaman lafiya a shiyyar ta arewa maso yamma da arewa ta gabacin najeriya
A nata jawabin a madadin matan gwamnan jihar, Dakta Badiyya Hassan Mashi ta tunato yadda Mata a jihar Katsina suka ci moriyar mulkin jam’iyyar APC tare karfafa masu gwiwar sake zaben ta domin maida biki
Tace sake zaben jam’iyyar ta APC yana nufin cigaba da amfana da salon mulkin da ta taho dashi na inganta rayuwar mata da matasan najeriya
Matan gwamnonin shiyyar sun tabbatar da cewa yan takarar jam’iyyar APC na tare da goyon bayan matan jihar Katsina da na shiyyar arewa maso yamma bisa abubuwan arzikin da suka samu daga salon mulkin jam’iyyar a jihar da kasa baki daya
Uwar gida Remi da Hajiya Nana Shettima sun samu rakiyar Ministar Kudi ta Najeriya Hajiya Zainab Shamsuna Ahmad da Ministar kasa a ma’aikatar Ciniki da Masana’antu Hajiya Zainab Katagum wadanda suka bayyana irin gudummuwar da APC ta bada ga rayuwar mata a najeriya ta hanyar shirye shirye da tsaren tallafi da shugaba Buhari ya bullo da su tare da kira ga matan da su zabi yan takarar APC domin dorewar shirye shiryen
Kazalika gangamin ya samu halartar shugabar matan jam’iyyar APC ta kasa da na jihohin shiyyar da dimbin mata da suka halarci taron
Wasu daga cikin matan da aka zanta da su a wajen taron sun jaddada goyon bayan su tare da alkawlin nemama yan takatar jam’iyyar ta APC goyon baya domin samun nasarar zaben na 2023 a dukkannin matakai.
Leave a Reply