Hukumar abinci ta duniya FAO tace akalla ‘yan Najeriya Miliyan 14.4 million suna fama da matsalolin karancin abinci.
Hukumar FAO, tace wannan adadi mutane dubu 385,000 wadanda suka rasa matsuguni ne ‘yan gudun hijira dake sansanin (IDPs) a jihohi 21 har da babban birnin tarayya Abuja.
Jami’in harkokin abinci na hukumar, FAO, Jasper Mwesigwa, ya sanar da haka a Abuja lokacin da aka gabatar da rahoto akan matsayi a Najeriya.
Hukumar FAO ta kara da cewa akalla miliyan 19.4 na ‘yan Najeriya zasu fuskanci karancin abinci da karancin kayan gina jiki daga watan Yuni zuwa Agusta na wannan shekara da muke ciki.
Jihohin sun hada da: Yobe, Barno, Kaduna, Katsina, Sakwato, Adamawa, Kano, Bauchi, Enugu, Naija a a Kebbi.
Sauran jihohin sun hada da Zamfara, Jigawa, Gwambe, Benuwai, Abia, Kuros Riba, Edo, Legas, Plateau da Folate.
Yace Wwannan headwear zatae Harmon zata karfafa samar da bayanai da suka dace kuma su kasance sun sanar da duk wani abunda zai auku akan lokaci ko shawarwarin da mash ruwa da team I suka dauka domin tabbatar da an Tanja kyakyawan shirin manufofi da shirye-shirye”.
LADAN NASIDI
Leave a Reply