Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Buhari Ya Ba Da Tabbacin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Yankin Arewacin Najeriya

Shehu Salman, Sokoto

0 248

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta lashi takobin sa kafar wando daya da dukkanin masu tada zaune tsaye a kasar musamman arewa maso yammaci bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashi kawo karshen dukkanin matsalolin tsaro da su ka addabi yankin yayin da ya ke jawbinsa a wajen bude babban taro na shekara-shekara da rundunar sojin kasa ta Najeriya ta gudanar a birnin Sokoto arewa maso yammacin kasar.

Taron da za’a kwashe kwanaki hudu ana gudanar da shi ya samu halartar manyan jami’an rundunar sojin kasa na Najeriya inda za’a gudanar da makaloli gami da yin bitar nasarorin ko akasin hakan da aka samu a bara da kuma shiri ga shekarar da ake tunkara, cikin nasarorin da aka samu a wannan shekarar ta 2022 sun hada da samar da wani sabon sashen jiragen sama na rundunar in ji babban hafsan rundunar Lafnar Janar Faruk Yahaya.

“Samar da sashen zai taimaka matuka wajen bayar da agajin gaggawa ga dakarun sojin kasa yayin da suke fagen daga gabanin isowar rundunar sojin sama wato Nigerian Air force, ya kuma zama tilas ayi aiki hannu da hannu idan har ana son haka ta cimma ruwa” in ji babban hafsan.

Baya ga babban taron, rundunar ta gudanar da bukin bude ayyukan da ta yi wa al’umma a mahaifar babban hafsan da suka hada da gina magudanan ruwa, makarantun firamare da karamar sakandire a gari Sifawa da kuma gina wurin saukar baki na Army Command Guest House a birnin Sokoto wanda gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar ya kaddamar.
Gwamnan ya yi godiya ga hukumar sojin tare da alkawalin ci gaba da bai wa rundunar dukkanin irin goyon bayan da su ke bukata daga gwamnatin ta jiha.
“Gwamnati da al’ummar jihar Sokoto na matukar godiya dangane da irin wannan karamci da rundunar sojin ta yi mana kuma gwamnatin na bayar da tabbacin ci gaba da kulawa da ayyukan da aka samar wa al’ummar jihar Sokoto a garuruwan Tangaza, Sifawa, Bodinga da kuma cikin kwaryar birnin na Sokoto” in ji Gwamna Tambuwal
Da ya ke jawabinsa a wajen bude taron, shugaba Buhari ya hori sojojin dasu tsame hannuwansu daga harkokin siyasa tare da jaddada alkawalinsa na gudanar da sahihin zabe a babban zaben kasar na shekara mai kamawa ta 2023.

Abdulkarim

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *