Domin samun ingantacciyar albarkatu a fannin noma a Nijeriya, ƙungiyar manoma ta Nijeriya, (AFAN), ta ba da shawarar saka hannun jari na gwamnati da na kamfanoni don tabbatar da ci gaba mai dorewa a harkar noma.
Da yake jawabi a wurin taron ciyar da Najeriya na 2022 (FNS), a Abuja, ranar Litinin, Shugaban AFAN, Alhaji Farouq Mudi, ya bukaci masu zuba jari na kasa da kasa da na cikin gida da su hada kai don gano damammaki da za su iya fassara don samar da aiki mai inganci da ci gaban kasuwanci.
A cewarsa, FNS wanda ake karbar bakuncin kowace shekara, yana ba da dandamali don yin aiki yayin da yake ba da mafita ga kalubale a aikin gona.
“AFAN a shirye take ta ba da tallafi bisa dabaru, da kuma saka hannun jari don cimma manyan manufofin ciyar da Najeriya 2022, ta hanyar zuba jari, injiniyoyi, sarrafa kayan noma, da kuma kera kayayyakin amfanin gona,” in ji Farouq.
Farouq ya bayyana cewa, rahoton hadin gwiwa da Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Dinkin Duniya FAO, Asusun Raya Aikin Noma ta Duniya, Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), Hukumar Lafiya ta Duniya da Majalisar Dinkin Duniya suka fitar. ya sanar da ci gaban da aka samu wajen kawo karshen yunwa da zurfafa nazari kan muhimman kalubalen da suka shafi hadafin.
Ya ci gaba da cewa rahoton na shekarar 2023 zai kawar da shakku kan ra’ayin cewa duniya na komawa baya a kokarin kawo karshen yunwa.
Leave a Reply