Jami’an tsaron kasar Gambia sun cafke wasu jami’an soji biyu da ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulkin da aka yi wa shugaba Adama Barrow a makon jiya.
Mutanen biyu, wadanda ba a bayyana sunayensu ba, an kama su ne a ranar Litinin.
A ranar 21 ga watan Disamba gwamnati ta ce ta kama wasu gungun sojoji dangane da yunkurin juyin mulkin.
Babbar kungiyar shiyyar yammacin Afirka, kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (Ecowas), ta yi tir da yunkurin juyin mulkin a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.
Leave a Reply