Take a fresh look at your lifestyle.

Babban mai gabatar da kara ya kaddamar da binciken tuhumar Shugaban kasa da Ministocin Peru

0 207

Babban mai shigar da kara na kasar Peru ya kaddamar da bincike kan shugaba Dina Boluarte da wasu manyan ministocin kasar a tsawon makonni da aka shafe ana gwabza fada da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

 

 

Ana binciken jami’an ne bisa zargin kisan kiyashi da kuma munanan raunuka. Tashin hankali ya barke bayan da aka kama tsohon shugaban kasar Pedro Castillo a watan Disamba saboda kokarin rusa Majalisar.

 

 

A ranar litinin mutane 17 ne suka mutu a rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan Castillo da jami’an tsaro a kudu maso gabashin kasar Peru. An jikkata wasu da dama a birnin Juliaca a ranar da ta kasance rana mafi muni da aka samu tashin hankali ya zuwa yanzu. Yawancin wadanda abin ya shafa sun samu raunukan harbin bindiga.

 

 

Hukumomi sun zargi masu zanga-zangar da yunkurin mamaye filin jirgin Juliaca da ofishin ‘yan sanda na yankin. Yanzu haka an kafa dokar hana fita na dare a yankin. A ranar Talata, ofishin babban mai shigar da kara ya sanar da yanke shawarar binciken Ms. Boluarte, Firayim Minista Alberto Otárola, da kuma ministocin tsaro da na cikin gida.

 

 

Shugaban kasar da ministocinta ba su fito fili su ce komai ba kan batun. Magoya bayan Castillo – wadanda yawancinsu matalautan ‘yan asalin kasar Peru ne – sun ce dole ne shugaba Boluarte ya yi murabus, a gudanar da zaben gaggawa, sannan a sake tsohon shugaban.

 

 

Mista Castillo, mai ra’ayin hagu, ya wallafa a shafinsa na twitter daga gidan yari, yana mai cewa ba za a taba mantawa da wadanda ke kare kasar Peru daga abin da ya kira juyin mulkin kama-karya ba. A wani ci gaba na daban a ranar Talata, gwamnatin Mr. Otárola cikin jin dadi ta sami nasarar kada kuri’ar amincewa da Majalisa.

 

 

Kasar Amurka ta Kudu ta shafe shekaru da dama tana tabarbarewar siyasa. Rikicin na baya-bayan nan ya zo

kan gaba a lokacin da Mista Castillo ya sanar da cewa zai rusa Majalisar da kuma kafa dokar ta-baci a watan Disamba.

 

 

Amma Majalisa ta kada kuri’a da gagarumin rinjaye don tsige shi.

 

 

Ana binciken tsohon shugaban ne bisa zargin tawaye da hada baki. Ya musanta dukkan zarge-zargen, yana mai jaddada cewa har yanzu shi ne halastaccen shugaban kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *