Hukumar kidaya ta kasa a Najeriya ta ce an tsara kidayar shekarar 2023 don samar da ingantattun bayanai, masu karbuwa kawai da bayanan kidayar jama’a masu amfani.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Hukumar, Malam Nasir Kwarra a yayin taron horar da manajoji da masu gudanarwa na matakin kasa na kwanaki uku , TCMA, don kidayar yawan jama’a da gidaje na shekarar 2023 a babban birnin tarayya Abuja.
#PhotoNews: Opening Ceremony of the National Level Training of the Training Centre Managers and Administration (TCMA) for 2023 Population and Housing Census held at the Public Service Institute of Nigeria, Abuja – 10th January 2023.#2023Census#YouCountBeCounted pic.twitter.com/LXhzCYVrJd
— National Population Commission (@natpopcom) January 10, 2023
Mista Kwarra ya ce: “Wannan yunkurin Zai samar da fa’ida da ingancin shirye-shiryen da aka yi na kidayar zuwa yanzu.
“Hukumar kidayar jama’a ta kasa ta himmatu sosai wajen sake rubuta tarihin kidayar jama’a a Najeriya tare da samar wa wannan kasa mai albarka ingantattun bayanan kidayar jama’a.”
Shugaban Hukumar ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su bi sahun hukumar a yunkurin baiwa kasar sahihan bayanai masu inganci ta hanyar kidayar yawan jama’a da gidaje na shekarar 2023.
“Shirye-shiryen ƙidayar yawan jama’a da gidaje na 2023 yana kan hanya kuma Hukumar tana da yakinin cewa hasashen ƙidayar gaskiya da aminci fiye da kowane lokaci.
“Wannan kyakkyawan fata ya samo asali ne daga gaskiyar cewa Hukumar yanzu ta dauki lokaci don ganowa tare da yin shawarwari kan batutuwan da suka dakatar da kididdigar da aka yi a baya kuma ta yanke shawarar kauce wa wadannan matsaloli ta hanyar amfani da tsarin kimiyya da fasaha na zamani.”
“Kidayar jama’a alhakin kowane dan kasa ne ya gabatar da kan shi don a kirga shi.”
“A cikin shekarun da suka gabata, Hukumar ta dauki lokaci mai yawa wajen tsare-tsare don samun nasarar gudanar da kidayar yawan jama’a da gidaje na 2023.
“Zaɓen a cikin shirin ya dogara ne akan amincewar da Hukumar ke da ita kan iyawar su don cimma abubuwan da ake tsammani.”
Leave a Reply