Take a fresh look at your lifestyle.

Daliban LAUTECH sun nuna goyon bayansu ga Gwamna Makinde

0 98

Daliban Jami’ar Fasaha ta Ladoke Akintola (LAUTECH) sun bayyana cikakken goyon bayansu ga sake tsayawa takarar Gwamna Seyi Makinde tare da yabawa Gwamnan bisa gagarumin nasarorin da ya samu a wannan makarantar.

 

 

Daliban sun ba da wannan yabo ne a yayin wani tattaki mai suna ‘Deserving Authority Walk,’ wanda hukumar kula da harkokin dalibai na kungiyar yakin neman zaben gwamna Seyi Makinde ta shirya wanda aka gudanar gabanin yakin neman zaben gwamnan a shiyyar Ogbomoso na jihar.

 

Tattakin da daliban suka gudanar, domin nuna godiya ga gwamnan kan yadda ya samu mallakin LAUTECH shi kadai, da rage kudin makaranta a makarantar da kuma soke kudaden da ba za a biya ba, babu tsarin jarrabawa da dai sauransu.

 

 

Tattakin ya samu halartar daliban LAUTECH, karkashin jagorancin shugaban kungiyar daliban jami’ar, Adeboye Anuoluwa; Kungiyar dalibai ta kasa (NANS), Zone D; NANS JCC, jihar Oyo da kuma majalisar kungiyar daliban Ogbomoso ta kasa da dai sauransu.

 

 

An fara Tattakin daga filin wasa na LAUTECH Amphitheater, ta ratsa yankunan Under-G, Stadium da Orita Naira inda aka kare a Oja’gbo, wurin taron kananan hukumomin Ogbomoso ta Arewa da Ogbomoso ta Kudu domin sake zaben gwamnan.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.