Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai tare da bayyana alhininsa game da mutuwar wasu Jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSCDC) guda bakwai da ‘yan bindiga suka yi musu kwanton bauna a jihar Kaduna a lokacin da suke bakin aiki.
Shugaban a cikin wani sako da ya aike, ya bayyana asarar jami’an NSCDC a matsayin wani lamari mai ban tausayi yayin da yake jinjina wa jajircewarsu da sadaukarwa ga al’ummar kasar.
Ya ce “Jami’an NSCDC wadanda suka jajirce wajen ganin sun kare kasarmu da al’ummarta sun yi sadaukarwa ta karshe wajen gudanar da ayyukansu.
“Tunanina yana tare da iyalan da suka mutu da kuma ’yan uwansu a hidimar. Allah Madaukakin Sarki Ya ba su da daukacin ma’aikata karfin gwiwar daukar wannan rashi,” inji shi.
Shugaban ya kuma umurci rundunar sojin kasar da su nemo tare da kamo ’yan bindigar da suka yi wannan barna.
Leave a Reply