Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya sabon zababben shugaban jamiyyar APC Abdullahi Adamu-lbayan babban taron da aka gudanar a babban Birnin tarayya Abuja
A cikin sakon taya murna,yace zaman jamiyyar tsintsiya madaurin ki guda itace hanr da zata hada kan ta tare da kasancewar Jamiyyar a sahun gaba wajen cin nasarar zabukan da zaa gudanar a shekara mai zuwa a Najeriya..
Shugaban ya halarci babban taron APC ne a Abuja tare da Mataimakin shi da Shugaban Majalisar tarayya wanda suke sa ran lashe zabukan bardi
“Wannan babban taron ‘ya’yan Jamiyyar APC da aka gudanar ya nuna karara cewa itace zatayi nasara a zabukan gama gari da zaa gudanar a shekara mai zuwa. An bai wa abokan gaba kunya saboda jita jitar da suke yadawa cewa kan jamiyyar ya rabu ,” inji Shugaban Kasa.
Da yake jawabi jim kadan bayan cin nasarar zaben, Shugaban jamiyyar APC, Abdullahi Adamu, ya alkawarta kyakyawan fata cewa jamiyyar APC zata taka rawar gani karkashin jagorancin shi
LADAN NASIDI
Leave a Reply