Dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Neja a arewa ta tsakiyar Najeriya, Umar Mohammed Bago ya kaddamar da yakin neman zabensa tare da yin alkawarin kammala dukkanin ayyukan raya kasa da tsohon gwamnan jihar ya kaddamar a fadin jihar.
Dan takarar gwamna wanda a halin yanzu dan majalisar wakilai ne mai wakiltar ChanChaga a jihar Neja ya bayyana haka a yakin neman zaben shiyyar Sanatan Neja ta Gabas a Kontagora hedkwatar shiyya.
Bago ya ce tsarin gwamnatinsa zai dogara ne kan kara yawan dukiyar jihar ta hanyar gina gadon magabata.
Ya ce gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali ne wajen magance tashe-tashen hankulan matasa ta hanyar karfafawa matasa da kuma ingantaccen ilimi domin samun karbuwa a cikin al’umma.
A cewar mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyyar Arewa ta tsakiya, Mu’azu Bawa, kimanin magoya bayan shi 4,780 ne suka sauya sheka daga sauran jam’iyyun siyasa zuwa jam’iyyar APC mai mulki a Kontagora.
” 87 daga cikin wadanda suka sauya sheka ‘yan jam’iyyar PDP ne, mata 261, maza 173 daga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP)”.
Leave a Reply