Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Kotun Kolin Habasha Tayi murabus

Maimuna Kassim Tukur,Abuja.

0 20

Shugabar kotun kolin Habasha, Meaza Ashenafi, da mataimakinta, Solomon Areda Waktolla sun yi murabus daga mukaminsu.

 

 

Rahoton ya ce wata wasika zuwa ga majalisar wakilai ta HPR ba ta bayyana dalilin murabus din nasu ba.

 

 

A halin da ake ciki, Majalisar ta amince da Mataimakin Farfesa Tewdros Mihret, daga Jami’ar Addis Abeba a matsayin Alkalin Alkalai, sai kuma Alkalin Kotun Koli ta Tarayya, Abeba Embiale, a matsayin Mataimakin Babban Jojin da ya maye gurbin Meaza da Solomon.

 

 

Babban mai shari’a Meaza da mataimakiyar ta Solomon PM Abiy Ahmed ne ya mika sunayensu ga majalisar wakilan jama’a ta HPR a ranar 01 ga Nuwamba, 2018. A yayin da dukkansu suka samu kuri’a bai daya daga majalisar.

 

 

Rahoton ya ce kwanan nan ne aka nada Solomon a matsayin alkalin kotun sauraron kararrakin zabe ta Majalisar Dinkin Duniya na tsawon lokaci na 2023-2030.

Leave A Reply

Your email address will not be published.