Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Buhari Ya Nemi Bitar MTEF Na 2022 Yayin Da Kasafin Kudi Ya Kai N7.35trn

0 458
Shugaban kasa Muhamadu Buhari ya aikewa majalisar wakilai wasika inda ya bukaci a sake duba tsarin kashe kudade na matsakaicin zango (MTEF) na shekarar 2022 wanda aka gina kasafin kudin bana.

A cewar wasikar da shugaban kasa ya aikewa shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila, gyaran ya zama dole domin an yi hasashen gibin kasafin kudin shekarar 2022 zai karu zuwa naira tiriliyan 7.35, wanda ya ke wakiltar kashi 3.99 na GDP. .

Shugaban ya ce karin gibin kasafin kudin za a samu ne ta hanyar sabbin rance daga kasuwannin cikin gida.

“Kamar yadda ka sani mai girma shugaban majalisar, sabon ci gaban da aka samu a fannin tattalin arzikin duniya da kuma na cikin gida ya sa a sake duba tsarin kasafin kudi na shekarar 2022 wanda aka gina kasafin shekarar 2022 a kansa. Jimillar gibin kasafin kudin ana hasashen zai karu da Naira biliyan 965.42 zuwa Naira tiriliyan 7.35 wanda ke wakiltar kashi 3.99 na GDP. Za a samar da kuɗin haɓakar haɓaka ta hanyar sabbin lamuni daga kasuwannin cikin gida. Bisa la’akari da gaggawar bukatar sake fasalin tsarin kasafin kudi na shekarar 2022 da kuma gyara kasafin kudin 2022, ina neman hukumar majalisar dokokin kasar da ta gaggauta daukar mataki kan wannan bukata.”

Shugaban majalisar bayan ya karanta wasikar ya mika ta ga kwamitin kudi na majalisar domin ci gaba da aiwatar da dokar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *