Take a fresh look at your lifestyle.

Hatsari: Shugaba Buhari Ya Ta’aziyya Da Tsohon Shugaban Kasa, Jonathan

0 379
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan bisa rasuwar ma’aikatansa guda biyu a wani hatsarin mota a cikin mako guda.

Shugaba Buhari ya bi sahun ‘yan kasar wajen yin addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu na taimaka wa tsohon shugaban kasar, ya kuma bukaci iyalan su da su ga rasuwar su a matsayin sadaukarwa ga kasa.

A cikin sakon, shugaba Buhari ya bayyana godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya sa shugaba Jonathan ya tsira daga hatsarin, inda ya bukace shi da kada ya shagaltu da tafiye-tafiyen da yake yawan yi a cikin gida da waje wadanda ke da alaka da samar da zaman lafiya a gida da waje.

Wasu ‘yan sanda biyu da ke tare da tsohon shugaban Najeriya sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota bayan da ayarinsa suka yi hatsari a hanyar filin jirgin sama na Abuja, ranar Laraba 6 ga Afrilu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *