Take a fresh look at your lifestyle.

Sakatariyar Baitulmalin Amurka Zata Ziyarci Afirka Ta Kudu

Theresa Peter,Abuja.

0 20

Sakatariyar baitul malin Amurka, Janet Yellen, za ta ziyarci kasar Afirka ta Kudu a mataki na baya-bayan nan na rangadin kasashe uku na Afirka da nufin bunkasa tasirin Amurka.

 

 

Ziyarar Ms. Yellen a Afirka ta Kudu na zuwa ne bayan ta ziyarci Senegal da Zambia.

 

 

Ziyarar a Afirka ta Kudu na zuwa ne a daidai lokacin da Washington ke fuskantar babbar gasa a yankin tare da Rasha da China.

 

 

A halin da ake ciki, a baya-bayan nan kasar Afirka ta Kudu ta karbi ragamar shugabancin kungiyar tattalin arzikin kasashen BRICS da ta kunshi Brazil, da Rasha, da Indiya, da kuma Sin.

 

 

Rahoton ya ce an kafa kungiyar ne a matsayin wata hanyar rage tinkaho ga mamayar da Amurka ke yi a duniya.

 

 

A yayin da take Afirka ta Kudu, ana sa ran Ms. Yellen za ta tura shugaba Cyril Ramaphosa don bin shirye-shiryen mika mulki sannu a hankali daga dogaro da makashin kwal zuwa makamashi mai tsafta.

Leave A Reply

Your email address will not be published.