Ziyarar ta kwana biyu wadda shugaban ya kai na da nufin kaddamar da wasu ayyukan raya kasa da gwamnatin jihar ta gudanar kalkashin jagorancin gwamna Aminu Bello Masari
Shugaba Buharin dai ya sauka a filin jirgin sauka da tashin jirage na tunawa da Marigayi shugaban kasa Umaru Yar’adua a daren jiya laraba inda ya samu tarba daga gwamnan jihar Aminu Bello Masari da mataimakinsa Mannir Yakubu da wasu daga cikin mukarabban gwamnatin jihar
A rana ta farko, ana sa ran shugaban kasar zai bude wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta gudanar domin inganta rayuwar al’ummar jihar
Daga cikin ayyukan da za zai kaddamar akwai aikin manyan gadojin kurde na kofar Kwaya da kofar Kaura a kwaryar birnin Katsina da aikin gyara da fadada babban asibitin Katsina
Akwai kuma aikin gadar sama na unguwar G.R.A. da cibiyar nazarin hasashen yanayi ta kasa watau Metrological Institute da sabon ofishin hukumar tara kudaden shiga na jihar
Kazalika, ana sa ran shugaban zai bude aikin samar da ruwan sha na kofar Kaura cikin birnin Katsina da kanfanin sarrafa shinkafa na Darma Rice Mill, wanda hamshakin dan kasuwar nan Dahiru Mangal ya gina.
Comments are closed.