Take a fresh look at your lifestyle.

Lalacewan Jirgi: Aikin Jirgin Kasa Daga Abuja-Kaduna Ya Cigaba

0 243

Hukumar Kula Da Zirga-Zirgar Jiragen Kasa ta Najeriya ta sanar da fara aikin titin jirgin kasa na Abuja Kaduna wanda aka dakatar a ranar Juma’a 27 ga watan Janairun 2023 sakamakon laluben da ya samu a tashar Kubwa a wannan rana.

Kamfanin Jiragen kasa ya dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna a wata Sanarwar da Daraktan Ayyuka, Mista Niyi Alli ya fitar ta ce za a ci gaba da aikin ne a ranar Talata 31 ga watan Janairu 2023 tare da jadawalin yau da kullun;

* KA2 zai tashi daga Rigasa a 0700

* Ak1 zai tashi daga Idu da karfe 10.00

*KA4 yana tashi RIGASA da ƙarfe 13.00

* AK3 zai tashi da karfe .16.00.

Sai dai a ranar Laraba kawai KA2 zaya tashi daga Rigasa a jihar Kaduna, a lamba 0700 da AK 4 za su tashi daga Idu a Abuja, da karfe 16.00.

Mista Alli a madadin Kamfanin ya sake neman afuwar abokan cinikinsa yana mai cewa, Kamfanin ya yi nadamar duk wata matsala da fasinjojin suka fuskanta sakamakon dakatarwar da aka yi na wucin gadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *