Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan kasar da su kasance masu kishin kasa Shugaban ya bayyana haka ne a gidan gwamnati dake Kano, a lokacin da yake liyafar cin abincin rana, bayan kaddamar da wasu manyan ayyuka takwas da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya aiwatar.
Ya dage cewa gwamnatinsa ta jajirce wajen yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram da ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a kasar nan.
“Mutane na iya ganin karara yadda wadannan kasashen ketare suka mamaye yankinmu mafi rauni na Najeriya, yankin tafkin Chadi, inda muke da arzikin danyen mai kuma suka haifar da mummunan tashin hankali a can, tare da kai hare-hare.”
Shugaba Buhari ya kara da cewa, a tafkin Chadi, idan ba jihar Borno tana da Gwamna irin Ummara Zulum ba, wanda yake Tsayin daka a kan aikinsa, da yanzu labarin ya sha bamban.
A cewarsa, a shekarar 2015 da ya karbi mulki a Borno kananan hukumomi da dama ne ke karkashin ikon ‘yan Boko Haram, “Kuma muna sane da cewa wasu na amfani da ‘yan tada kayar baya wajen haddasa matsala, amma a yau yawancin kananan hukumomin sun samu ‘yanci. .”
Shugaban ya koka da yadda masu ruguza jihar Borno, suna amfani da Boko Haram sun san cewa Borno kasa ce mai karfin arziki, “Shi ya sa lokacin da nake Gwamna a can na je Nijar da Chadi har ma da Kamaru saboda kuna bukatar Makwaftan ku su tsira.”
Shugaba Buhari ya yabawa gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan ci gaban da ake samu a jihar. Ya kuma yabawa Gwamnonin jihohin Legas da Kaduna da Katsina da kuma Kogi bisa yadda suka nuna bajinta wajen ganin an samu rabon dimokuradiyya a yayin da ya bukaci masu ruwa da tsaki da su taimaka wajen bunkasa ilimin matasa wadanda ya bayyana a matsayin masu rike da madafun iko, inda ya nuna cewa rashin ilimi na haifar da matsaloli a al’umma.
Leave a Reply