Kungiyar kasa da kasa mai kula da Ingancin abubuwa ta amince da ingancin tsarin gudanar da aiyyuka na Ofishin Shugabar Kula da Mai’ikatan Gwamnatin Najeriya.
Shugabar Maaikatan Gwamnatin Najeriya , Folashade Yemi-Esan tace wannan bukin na daga cikin abubuwan da yi domin gudanar da garambawul din Maaikatan Gwamnati a Najeriya.
Tace wannan tsarin ISO 9001:2015 shine mafi karbuwa mai inganci a idon duniya da ya samar da kyakyawan tanadi da kungiyar ke bukata domin taimaka wa bukatun masu ruwa da tsaki akai akai wajen garambawul da ci gaba da bunkasa.
“Abun muhimmanci na tsarin ISO 9001:2015 QMS amincewar ofishin Shugabar kula da Maaikatan Gwamnatin Najeriya domin karfafa ci gaban inagancin aiyyukan ma’aikata da zai dace da na sauran kasashen duniya”.
Ta tunatar da cewa nuna goyon bayan ISO 9001:2015 na nufin ci gaba da gudanar da tsarin har na tsawon shekaru uku kuma ofishin Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Najeriya shine Ma’aikata ta farko da zata ci gajiyar wannan tsari a tsakanin ma’aikatu.
Yemi-Esan ta bukaci a hada karfi da karfe wajen tabbatar da ci gaban ingancin QMS har na tsawon shekaru uku.
Tun da farko a jawabinta Manajan Daraktar, Digital Jewels Africa, Mrs. Adedoyin Odunfa, ta sanar da cewa makasudin zabar ofishin Shugabar Ma’aikatan Gwamnati a wanna tsari shine bin hanyoyin tabbatar da ingancin aiki ga masu ruwa da tsaki domin kawo wani sauyin aiki ga kasa baki daya.
“Tsarin ISO9001 ya kuduri anniyar ci gaban tsarin QMS a kungiyance da zai ci gaba da samar da kyakyawan tsari mai dorewa domin cimma bukatun masu ruwa da tsa da kwastomomi dake bin kaidojin kungiya”, a cewar Odunfa
Hakazalika wakilin Shugaban gidauniya, Aig-Imoukhuede, wani bangaren dabarun aiki OHCSF, Mr Pattison Boleigha, yace wannan amincewar tsarin ISO 9001:2015 QMS hanya ce da zata baiwa Ma’aikatan Gwamnatin Najeriya damar ci gaba.
Leave a Reply